A yau Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Ministocin sa 43, tare da yi musu umarnin rage kashe kudade, daina zuruttun zuwa ganin sa, sai dai su fara neman bukatar ganin sa ta hannun Abba Kyari, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa tukunna.
Shugaba Buhari ya ce ko kasashen waje kada Ministoci su kara tafiya ba tare da sanin Fadar Shugaban Kasa ba.
Buhari ya kuma hore su da yin aiki tukuru tare da taimaka a fitar da talaka milyan 100 a cikin kangi da kuncin talaucin da ya ce ke damun ‘yan Najeriya.
Lokacin da Buhari ya hau mulki a 2015, sai da ya shafe watanni shida kafin ya nada sabbin ministoci. Kafin sannan ‘yan jarida sun tambaye shi dalilin da ya sa ya ki nada ministoci da wuri, sai ya ce ai ba wani aiki suke yi ba, banda surutai kawai.
Kafin ya nada su, ya ce ministocin Jonathan sun yi yawa, inda ya ce shi kuma ya rage, ya dauki 37 kawai. Sai dai kuma a yanzu da Buhari ya sake hawa mulki karo na biyu a 2019, ya nada ministoci har 43, fiye ma da wadanda Jonathan ya nada.
Kafin nada ministoci a wannan karo, Buhari ya fito ya ce ba zai nada kowa ba, sai wadanda ya sani, kuma ya tabbatar da cewa sahihai ne nagari. Sai dai kuma sunayen ministocin da ya fitar sun bar baya da kura, ganin a cikin su akwai wadanda ke da tabon zargin wawurar dukiyar Najeriya da dama. Sannann kuma akwai wadanda ba a san yadda aka yi Buhari zai iya kafa hujja da kyakkayawan sanin da ya ce ya yi musu ba.
Sannan kuma Buhari ya maida wasu ministoci kan mukaman su na da inda ‘yan Najeriya da dama suka rika korafi da kuka da su.
Abin lura kawai shi ne yadda aka rage wa Minista Raji Fashola nauyi, aka raba shi da ma’aiakatu biyu daga cikin uku, aka bar masa daya tilo. Sannan kuma da sake dora ministan Abuja da ake ganin ba shi da wayewar tsara babban birnin tarayya kamar yadda yake a wasu kasahen da suka ci gaba.
A wancan karon yan Najeriya sun yi korafi da dama game da yadda tsohon ministan Ayyukan gona yake gudanar aiki a ma’aikatar.
Babban abin da aka fi cecekuce akai kuwa shine zamani ya yi masa nisa da irin yanzu ba irin noman da ya sani bane ake yi. An bukaci Bubari da ya nada matashi ne da zai iya bunkasa fannin.
Sai dai kuma anan ma bata canja zani ba domin Minista Nanono da aka nada shima ba na yau bane. Da kamar dai za aci gaba da gashi ne kawai.
Yanzu fa kimiyya da fasaha sune ake attukan gona da su tuni an wyce fartanya da garma.
Cikin wadanda ba ta canja zani ba din akwai:
Muhammad Musa Bello (Adamawa) – Abuja
Chris Ngige (Anambra) – Kwadago
Adamu Adamu (Bauchi) – Ilimi
Ogbonnaya Onu (Ebonyi) – Ministan Kimiyya da Fasaha
Geofery Onyeama (Enugu) – Harkokin Kasashen Waje
Zainab Shamsuna Ahmed (Kaduna) – Kudi
Hadi Sirika (Katsina) – Jiragen Sama
Abubakar Malami (Kebbi) – Shari’a
Lai Mohammed (Kwara) – Yada labarai
Babatunde Raji Fashola (Lagos) – Ayyuka
Rotimi Amaechi (Rivers) – Sufuri