Mijina kan danne ni da karfin tsiya ne idan yana so ya sadu da ni – Matan Aure

0

Wata matan Aure mai suna Charity John ta nemi kotu ta raba aurenta da mijin ta cewa wai yana nemanta a gado da karfin tsiya a duk lokacin da yake bukatarta.

Charity da ke zaune da Mijinta a Unguwan Jikoyi dake, Abuja ta ce baya ga danneta da karfin tsiya da yake yi, mijinta Abel manemin mata ne.

” A duk ranar da yake bukata ta da karfin tsiya yake danne ni don samun abinda yake so. Kuma shi haka yake yi kullum. A dalilin haka nake rokon kotu ta raba auren mu kawai in huta.

Abel ya ce Karya ne matan shi take yi.

” Ban taba neman matata da karfin tsiya ba, sharri kawai take yi min. Ina so in gaya muku cewa ita ce ke neman maza ma domin na taba ganin tana yi wa wani dan chana karyar cewa zata aure shi sannan wai bata da miji.

Abel ya bayyana wa kotu cewa shima fa auren ya ishe shi hakanan. Araba kawai.

Alkalin kotun ya dage karar zuwa ranar 26 ga watan Agusta.

Share.

game da Author