Matawalle ya cancanci yabo, ina yaba masa matuka – Inji Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tabbas dole ne a fito a rika jinjina wa gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle saboda jajircewa da yayi wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar.

Buhari ya bayyana haka ne da yake karbar bakuntar sarakunan yankin Arewa da suka ziyarce shi a fadan shugaban kasa karkashin jagirancin sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar III.

” Ina kira ga gwamnatocin jihohin kasarnan da su yi koyi da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kan yadda ya maida hankali wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar Zamfara da kuma irin matakan da yake bi domin samun nasara a kai.

” Matawwalle Ya nuna kishi matuka da son zaman lafiya a jihar ta hanyar hada kan mutanen jihar.”

Sake fasalin ‘Yan sanda

A wannan taro da shugaba Buhari yayi da sarakunan ya bayyana musu cewa tabbas gwamnatin sa za ta yi tankade da rairaya sanan zata gyara fasalin rundunar ‘yan sandan Najeriya.

” Baya ga haka tuni mun mika wa hukumomin da ke da ikon bada lasisin iya mallaka da amfani da naura mai tuka kansa (Drone) domin hango maboyan miyagun mutane a dazuka.

” Sannan kuma zamu saka naura mai daukan mutane a manyan titunan kasar nan domin tona asirin masu aikata tsiyaa hanyoyin mu da fazuka.

” Buhari ya yi kira ga sarakunan da su taimakawa gwamnati bisa wannan abu da tasa a gana domin samun nasara a kai.

Buhari yace ya yi irin wannan ganawa da sarakunan yankin kudu akan irin haka.

Share.

game da Author