Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Simon Achuba, ya zargi Gwamna Yahaya Bello da rura wutar tashe-tashen hankula a jihar.
Da ya ke magana a wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels, Simon Achuba ya ce gwamnan Yahaya Bello na yi masa bi-ta-da-kulli, dukan kabarn kishiya, don kawai shi mataimakin ya na yin abu “yadda ya kamata a rka yin sa.”
Daga nan kuma ya yi kira a kara tsaurara tsaro a Kogi, saboda fantsamar rikice-rikice a ake fama a shi a jihar.
“A matsayi nan a mataimakin gwamna, ina bakin kokari na ga na yi aiki na da kuma komai a bisa yadda ya dace. A kan haka ne ya tsane ni kuma ya hana ni hakkoki na.
“Dalili kenan a taro da na yi na baya da manema labarai na yi kuka duniya ta sani cewa jami’an tsaro su sa ido sosai a kan jihar Kogi. Saboda wutar rikicin da gwamnan Kogi ke rurutawa.” Inji Mataimakin gwamnan.
Ya bayyana cewa ba shi wata hulda da gwamnan, sai ma kuntata masa da ya ke yi. Ga shi kuma kamar yadda ya bayyana, gwamna Bello ba ya bin tsarin yadda ake tafiyar da ingantacciyar gwamnati. Sannan kuma bai tsinana wa al’umma komai a jihar ba.
Achuba ya ce gwamna Bello gaba-gadi kawai ya ke mulkin sa, ba tare da ya natsu ya bi turbar da ta dace ba.
A cewar sa, Gwamna Bello bai aminta da a rika sukar sa ba. Wannan kuwa ba ce turba ta kwarai da mai shugabancin al’umma zai rike ba.
“Idan za ka yi nazarin gwamnatin Yahaya Bello tun daga ranar da ya hau mulki har zuwa yau, fada kawai ya ke yi da duk wanda ya kawo masa wani ra’ayi da ya kauce wa ra’ayin sa. Daga nan ka zama abokin gabar sa.
A karshe ya ce duk da gwamnoni da sarakunan gargajiya sun shiga cikin sabani da tauye hakkin da gwamna ya y i masa, har yanzu Bello bai nabba’a ba. Bai daina kuntata masa ba.
Discussion about this post