Masu garkuwa sun arce da malamin Jami’a a Kaduna

0

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya bayyana cewa masu garkuwa sun arce da wani malamin Jami’ar gwamnatin Tarayya dake Dutsinma, Katsina.

Wanda aka yi garkuwa da, Abubakar Idris mazaunin unguwar Barnawa ne dake Kaduna.

” DPO na unguwar Barnawa ne ya sanar da mu abinda da ya faru cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun tafi da Abubakar Idris a gidansa dake titin Lawal Ahmed, Barnawa Kaduna.

” DPO ya ce ko kafin su isa wurin masu garkuwan sun tafi da shi. Sai dan an gano cewa masu garkuwan sun biyo shi ne tun daga wani wuri har zuwa gidansa da wajen karfe ɗayan dare.

Sabo ya ce tuni har su tura ma’aikata su bi sawun waɗannan masu garkuwa.

Share.

game da Author