Likitocin jihar Barno sun janye shirin fara yajin aiki

0

A ranar Litini ne likitocin dake aiki a asibitin Ƙwararru a Maiduguri jihar Barno suka sanar cewa sun janye shirin fara yajin aiki da suka ƙudiri farawa ranar biyar ga watan Agusta.

Mathew Aristotle wanda ya jagoranci zaman sasanta likitocin da hukumar asibitocin ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a Maiduguri.

Aristotle ya bayyana cewa likitocin sun shirya fara yajin aiki ne ranar biyar ga watan Agusta saboda rashin biyan su albashi da alawus alawus na tsawon watanni takwas da ba a yi ba.

Bayan haka ya kara da cewa Aristotle yace an samu daman samun matsaya ne bayan kungiyoyi da dama sun saka baki domin shawo kan matsalar.

Ya ce a dalilin haka kuwa aka baiwa hukumar asibitocin wa’adin kwanaki biyar wato daga ranar biyar zuwa tara ga watan Agusta domin biyan albashi da alawus alawus ɗin likitocin asibitin.

Sannan sun kuma miƙa godiyar su ga gwamna Zulum bisa kokari da yake yi wajen ganin an wanye lafiya a tsakanin likitocin da mahukuntan asibitocin.

Share.

game da Author