Kamar yadda kowa ya sani cewa nan da rana ita yau sai dai arika yi wa juna gaisuwar Anyi Sallah Lafiya? Kasuwannin raguna sun cika makil a ko ina a fadin Kasar nan.
Sai dai kuma duk da cikar su ana samun karancin masu siya.
Babban dalili kuwa shine na cika buri da masu ragunan suka saka akan dabbobin su.
Gaba daya basu tabuwa saboda tsadar da suka yi.
A wasu Kasuwanni da aka garzaya domin saninnko ya cinikibya ke kayawa a bana, masu raguna suna ta kokawa da karancin masu siya.
Wani Malam Bello dake kasuwar ‘Yan tumaki dake garin Kaduna ya ce a gaskiya ana samun karancin masu garzayowa domin siyan rago duk da sallah ta karato.
” Abin da zan ce anan shine har yanzu dai akwaibsauran lokaci domin wasu suka siya rago ne idan ana gobe Sallah. Ba mu cire tsammanin za mu yi ciniki ba tukuna.
Ya kara da cewa har yanzu ana ta shigo da raguna ne jihar.
A wasu jihohin da wakilin mu ya tambaya, abin bai sake zani ba da yadda yake a Kaduna.
Wakilin mu ya tattauna da mutane da dam game da shirin sallar layyan inda da yawa suka shaida masa cewa tsadar raguna ne yasa suka dan dakata tukunna kafin ko farashin subzai yi sauki.
” Ragon da aka siyar 25,000, a bara yanzu yakannkai har 45’000. Ka ga ko ta yaya talaka zai iya yin layya? Ba ragon bane, akwai abinci da sauran hidindimu da za ayi a wannan lokaci.” Inji Abdullahi.
Yanzu dai duk inda ka waiwaya za ka ga raguna jibge ana an farautar masu siya.
Discussion about this post