KWALLON KAFA: Van Dijk ya lashe kyautar Gwarzon Zakaran Turai

0

Mai tsaron bayan Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool FC, Virgil van Dijk, ya zama Gwarzon Zakaran ‘Yan Kwallon Turai.

UEFA ce ta bayyana sunan sa a yau Alhamis, bayan da ya doke Leonel Messi da Cristiano Ronaldo a rukunin maza, a birnin Monaco, kasar Faransa.

Dan asalin kasar Natherland, Dijk ya ci wa kungiyar kwallaye 9 tare da buga wasanni 59 a kakar 2018/2019.

A cikin kakar wasanni ta 2018/2019, har ila yau, Dijk ya buga wasanni na tsawon mintina 4,465, kwatankwacin wasanni 50, ba tare da wani dan wasa ya yanke shi ko ya kwace kwallo a hannun sa ba.

Wasanni 50 ya buga a jere ba tare an samu baraka ta hannun sa an keta masu tsaron bayan Liverpool ba.

Dijk ya taimaka wa Liverpool matuka wajen kai kungiyar ga samun nasarar lashe Kofin Zakarun Turai na 2018/2019, inda ta doke kungiyar Tottenham a wasan karshe.

A shekarar gasar da ta gabata kafin 2018/2019 ma kungiyar ta kai ga wasan karshe, inda ta sha kashi a hannun Real Madrid.

Har ila yau kuma a yau ne UEFA ta fitar da rukuni-rukuni na gasar Kofin Zakarun Turai, wato Champions League na kakar 2019/20120 duk a Monaco din.

GROUP A

PSG

Real Madrid

Club Brugge

Galatasaray

GROUP B

Bayern Munich

Tottenham Hotspur

Olympiacos

Crvena Zvezda

GROUP C

Manchester City

Shakhtar Donetsk

GNK Dinamo

Atalanta

GROUP D

Juventus

Atletico Madrid

Bayer Leverkusen

Lokomotiv Moskva

GROUP E

Liverpool

Napoli

Salzburg

Genk

GROUP F

Barcelona

Borussia Dortmund

Inter Milan

Slavia Praha

GROUP G

Zenit St. Petersburg

Benfica

Olympique Lyon

RB Leipzig

GROUP H

Chelsea

Ajax

Valencia

LOSC Lille

Share.

game da Author