Kotu ta wanke hadimin Jonathan daga zargin harkallar bilyan naira 1.6

0

Bayan ‘yan adawa sun shafe shekaru hudu su na kiran sa ‘barawo’, a karshe dai Babbar Kotun Tarayya da Legas ta wanke Tsohon Hadimin Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, mai suna Warimapo-Owei Dudafa daga zargin wawurar naira bilyan 1.6.

Babban Mai Shari’a, Mohammed Idris, ya ce mai gabatar da kara, wato Hukumar EFCC ta kasa gabatar da kwakkwarar shaida da hujjojin da kotu za ta kama Dudafa da laifin harkallar naira bilyan daya da milyan dari shida da suke zargin sa da aikatawa.

Tun cikin 2016 EFCC ta caji Dudafa, wanda masanin harkokin banki ne da kuma wani mai suna Joseph Owuejo da laifin karkatar da makudan kudaden.

Mai Shari’a Idris ya ce kasawar da EFCC ta yi ta gabatar wa kotu da hujjoji na zahiri da na badini, sun nuna kamar ita EFCC din ta na da hujjojin, amma ba ta son bayyana wa kotu.

“ Zargin tabka manyan laifuka kamar sata da zamba abu ne da dokar kasar nan ke dogara da hujjoji kwarara kafin ta kama wanda ake zargi.

“Amma zargi, shaci-fadi da kakale-kakale ko kame-kamen bayanai domin sarkafa wa wanda ake zargi laifi, to wannan baa bin amincewa ba ne a kotu.” Inji Mai Shari’a Idris.

“A zahiri EFCC ba ta shirya ba, kuma a bisa hujjojin da suka gabatar wa kotu, sun nuna ba su ma yi kwakwaran bincike kan wanda suke zargi ba, kafin su garzayo kotu su maka shi gaban shari’a, domin a hukunta shi.

“Saboda ita kotu ba ta amsa ji-ta-ji-ta, shaci-fadi, an-ce-an-ce ko kame-kame a matsayin kwakkwarar hujja.

“Maganar gaskiya kawai dai EFCC ta maida hankali ne wajen kamo-can-kamo-nan a matsayin hujjar da ta ke so kotu ta hukunta wanda ta ke zargi.

“Bari na kara yin dalla-dalla. Kotu ba ta ce sai mai gabatar da kara ya kawo hujjojin shaidu na mutane ba. Amma shi mai gabatar da kara ya na da nauyin tilas fa sai ya kawo hujjoji ba kwafe-kwafen takardun bayanai da kotu za ta iya amfani da su ta kama wanda ake zargi da laifi.

Sannan kuma ya ce kasa gabatar da wasu shaidu hudu da EFCC ta yi ya kara kashe kaifin zargin da hukumar ke yi wa Dudafa.

Share.

game da Author