Kotu ta tsare mahaifin da ya dirka wa ‘yarsa ciki

0

Kotu a Jihar Oyo ta tsare mahaifin da ya dirka wa ‘yarsa ciki.

Mahaifin mai suna Emmanuel Ikhine mai shekaru 52 ya rika yin lalata da ‘yar cikin sa ne a duk lokacin mahaifiyarta bata nan kuma kanninta maza basu gidan.

Da abin ya ishi wannan yarinya ne sai ta garzaya gidan wata mata da ke makwabtaka da su ta fada mata abinda ke faruwa.

Yarinyar ‘yar shekara 18 tace a duk rana sai mahaifinnata ya nemeta a gado.

Bayan Kotu ta saurari wannan kara sai ta aika da yarinyar asibiti domin a duba lafiyarta.

A nan ne aka gano cewa ashe ma tana dauki da cikin mahaifin nata.

Yanzu dai kotu ta ce ‘yan sanda su ci gaba da tsare wannan magidanci har sai an kammala bincike.

Share.

game da Author