Kotun dake sauraren kararrakin Zaben majalisar dattawa na jihar Kogi ta soke zaben sanata Dino Melaye a matsayin sanatan dake wakiltar Kogi ta Kudu.
Alkalin Kotun ya yanke hukuncin a sake zabe a wannan shiyya.
Idan ba a manta ba, dan takarar kujerar na jam’iyyar APC, Smart Adeyemi ya shigar da kara a kotun yana kalubalantar Zaben Dino.
Sai dai shi sanata Dino yanzu ba ta kujerar Snata yake ba, tuni ya mike yana ta zabga Kamfen din zama gwamnan jihar Kogi.
Yana yawon Kamfen ne domin samun amincewar deliget din PDP su zabe shi dan takarar jam’iyyar.