Kotu ta bada belin El-Zakzaky

0

Kotu a Kaduna ta ba belin shugaban ƙungiyar IMN, Shiite, Ibrahim Elzakzaky da matarsa Zeenat.

Alkalin kotun ya ce El-Zakzaky zai tafi ƙasar India domin a duba lafiyar sa tare da matarsa da wasu jami’ai.

An bayyana cewa El-zakzaky zai tafi asibitin Asibitin Mandeta da ke, New Delhi a India.

Idan ba a manta ba daure El-zakzaky da matar sa Zeenat in a shekarar 2015 bayan arangama da Ƴan Ƙungiyar suka yi da tawagar babban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai.

Magoya bayan sa sun yi da yin zanga-zangar a faɗin kasar nan suna kira da a saki shugabansu.

Share.

game da Author