Kotu ta ɗaure malamin Islamiyyan da ya rika yin lalata da ɗaliban sa maza

0

A ranar Litini ne kotun majistare dake Kontagora jihar Neja ta yanke wa wani malamin Islamiyya Abubakar Abdullahi mai shekaru 33 hukuncin zama a gidan yari har na tsawon shekaru bakwai a dalilin kama shi da laifin yin lalata da dalibansa maza 35.

Alkalin kotun Hauwa Yusuf ta kuma bai wa Abdullahi zabin biyan kudin belin Naira miliyan biyu bayan ya kamala yin shekaru hudu daga cikin shekaru bakwai a kurkuku.

Dan sandan da ya shigar da karan Daniel Ikwoche ya bayyana cewa wani ma’aikacin kungiyar Hisbah dake karamar hukumar Kontagora mai suna Murtala Abdullahi ne ya kai karan aika- aikan da Abdullahi ya aikata ofishin ‘yan sanda ranar 22 ga watan Yuli.

Yace Abdullahi wanda mazaunin Sabon garin Kontagora ne ya rika danne yaran da yake karantarwa a ɗakin sa a kusan kullum yana lalata da su ta baya.

Waɗannan yara duk basu wuce shekaru 9 zuwa 14 ba.

Da alkali Hauwa ke karanta hukuncin da kotu ta yanke masa Abdullahi ya amsa laifin da ya aikata sannan ya roki kotun ta yi masa sassauci.

Idan ba a manta ba ko a kwanakin baya da suka wuce mun ruwaito rahoton yadda wasu Iyayen yan mata uku masu shekaru 7 zuwa 12 suka maka wani malamin Islamiyya a jihar Legas bisa zargin yin lalata da ƴaƴansu a makaranta.

Share.

game da Author