Hukumar ’Yan Sanda ta kara ruruta caccakar da dimbin jama’a ke wa sojoji, dangane da kisan zaratan ‘yan sandan da ke faraytar masu garkuwa da mutane, cewa babu wata hujjar da za su fito su shaida wa duniya cewa ita ce ta sa suka kashe ‘yan sanda uku a Jihar Taraba.
Yadda Sojoji suka bindige Zaratan ‘Yan sandan da Najeriya ke tunkaho da su
“Amma a daidai kan hanyar su ta zuwa Jalingo tare da babban mai garkuwa da mutane daure a cikin ankwa, wajejen tsakanin Ibbi zuwa Wukari, sai zaratan ‘yan sandan su 10 su ka ji sojoji sun bude musu wuta da harbi. Sojoji a cikin wata farar mota bas su ke. Sun kashe ‘yan sanda uku da farar hula daya. Wasu da yawa kuma suka ji ciwo.
“Daga nan sai sojojin suka kwance wa mai garkuwa da mutanen ankwa suka sake shi.
Duk da cewa an kafa kwamitin bincike, rundunar ‘yan sanda ba ta gamsu da irin yadda ba a dauki batun da muhimmancin da ya kamata a ce an dauke shi ba.
Wannan ne ya sa jiya Alhamis Kakakin ‘Yan sanda Frank Mba ya ragargagi sojoji saboda sun ce wai sun bude wa ‘yan sanda wuta ne, saboda sun yi zaton masu garkuwa da mutane ne. Kuma sun yi hakan ne bayan da aka kira su aka sanar da su cewa an yi garkuwa da wani.
Wanene ne Alhaji Hamisu, gogarman mai garkuwa da ya tsere?
Sunan sa Alhaji Hamisu Bala Wadume, rikakken mai garkuwa da mutane ne wanda ya yi mummunan kaurin suna wajen karbar makudan milyoyin kudade daga wanda ya yi garkuwa da su.
Kwanan nan aka biya Alhaji Hamisu diyyar fansar wani hamshakin attajiri mai harkar man fetur zunzurutun kudade har naira milyan 100 a Jihar Taraba.
Tambayoyi 15 da ‘Yan sanda ke neman amsar su wajen Sojoji dake musanta kisan da suka yi
Tambaya ta farko kuma mai muhimmanci it ace, shin ina Alhaji Hamisu Bala Wadume, miloniyan mai garkuwa da mutane wanda ‘yan sanda suka kama, suka sa masa ankwa?
Idan shi ne sojoji ke zaton an sato shi har suka je ceton sa, to ya aka yi suka same shi da ankwa?
Me ya sa ba za su yi bincike ba sai kawai su kwance masa ankwa su sake shi?
Wane ne ya kira su ya shaida musu cewa masu garkuwa sun saci wani sun gudu da shi, alhali kuwa ‘yan sanda ne suka kama mai garkuwa suka saka masa ankwa?
Me ya sa ba su kama wanda suka wai shi ne ya kira sojoji ya ce musu ga shi can an yi garkuwa wa wani ba.
Kuma wane mutum ne aka fada wa sojojin cewa an yi garkuwa da shi, alhali su ‘yan sanda mai garkuwa da mutane suka kamo?
Karya ne da aka ce wai ‘yan sanda ba su bayyana musu cewa su jami’an tsaro ba ne. domin bidiyon da ake watsawa a soshiyal midiya ma za a ji har wani soja na fada da karfi cewa ‘yan sandan daga Hedikwatar Abuja suke.
Ba gaskiya ba ne da aka ce hukumar ‘yan sanda ba ta sanar da jami’an ta daga Abuja za su ce Taraba kamo mai garkuwa da mutane ba. Sun je hedikwatar ‘yan sanda ta Jalingo sun kai rahoto, kuma sun je Ofishin Shiyya na Wukari sun kai rahoton cewa an turo su Taraba su yi kame. Hatta jami’an CID na Taraba ma da su aka je kamen.
Hukumar ‘Yan Sanda a Abuja ta bayyana bayanin da sojojin Bataliya ta 93 da ke Takum suka yi da suka ce sun dauka masu garkuwa ne, cewa rashin mutunci ne da kuma rashin kyautawa karara.
Shin ta yaya suka saki Alhaji Hamisu suka bari ya gudu?
Ta yaya aka yi mutumin da ke daure da ankwa zai tsEre daga hannun sojoji, su da suka ce wai ceton sa suka je, sun dauka sato shi aka yi?
Idan sojoji sun ce sato Alhaji Hamisu aka yi suka kubutar da shi, to ina suka kai shi domin kare lafiyar sa?
Me ya sa ba su kai shi Sansanin Sojoji an rubuta shi a cikin rekod na wadanda hukuma ta kwato daga hannun masu garkuwa, kamar yadda ake a ka’idance ba a tsarin aikin soja?
Me ya sa sojoji suka hah-harbe su a daidai lokacin da suka iske su, duk da cewa sun nuna musu cewa su ‘yan sanda ne?
Zaratan da aka yi babban rashin su
Wata sanarwa da hukumar ‘yan sanda ta fitar da baya, ta bayyana cewa zaratan jami’an tsaron da aka kashe sun a daga cikin wadanda suka kubutarcda Magajin Garin Garin Daura, wanda ya shafe watanni biyu cur a hannun masu garkuwa.
Kuma da su aka kamo rikakken mai garkuwa da mutane nan a Lagos shekaru biyu da suka gabata, mai suna Evans.
Akwai Insifeto Mark Edaile, Sajan Dhiru Musa da kuma Sajan Usman Dan-Azumi.
Buhari ya ce a binciki yadda aka kashe ‘yan sanda uku
Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin a gaggauta binciko yadda aka kashe zaratan ‘yan sandan uku wadanda ke cikin jami’an tsaron da aka tura Jihar Taraba daga Abuja, domin su kamo rikakken attajirin nan mai garkuwa da mutane, Alhaji Hamisu Bala Wadume.
Sojoji ne dai suka bude musu wuta, tare da kashe uku, sannan kuma suka saki mai garkuwar, wanda aka kamo kuma a lokacin ya na cikin ankwa.
An kamo Hamisu Bala bayan a kwanakin baya ya karbi naira Milyan 100 cur domin ya saki wani attajiri mai harkar man fetur da ya yi garkuwa da shi a Taraba.
A yanzu dai Hamisu ya gudu, ba a san inda ya ke ba.
Discussion about this post