KISAN ƳAN SANDA: An umarci sojoji rika hattara da kaffa-kaffa da ƴan sanda

0

Hukumomin Tsaro na Sojoji sun fitar da sanarwar cewa jami’an sojoji su rika kaffa-kaffa da yin taka-tsantsan a duk inda suka ci karo da jami’an Ƴan sanda.

Umarnin ya ce su rika yin kaffa-kaffa a makonnin nan masu zuwa, a duk inda suka ci karo da ƴan sanda a fadin kasar nan.

Wannan umarni ya biyo bayan caccakar da sojojin Najeriya ke sha a fadin kasar nan bayan bindige zaratan ‘yan sanda da sakin rikakken dan fashi da garkuwa da mutane a Jihar Taraba.

Ƴan sanda sun ce da gangan sojoji su ka yi musu kwanton bauna, suka bi su, sannan su ka bude musu wuta da nufin kubutar da Alhaji Hamisu Wadume da ‘yan sanda suka kamo a cikin ankwa.

Sojoji sun kubutar da shi kamar yadda ƴan sanda suka yi zargi, bayan sun kamo shi sakamakon farautar da shekaru da dama da suka rika yi.

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira cewa kowa ya maida wukar sa a cikin takobi, ya kuma bada umarnin cewa a gaggauta yin binciken hakikanin abin da ya faru.

Ranar Lahadin jiya da ta gabata ne kuma sojoji suka fitar da wasu shawarwari da umarni ga daukacin jami’an su cewa su rika in hattara, kamar yadda aka fitar da wannan sanarwa a soshiyal midiya, ba tare da umarnin a fitar da ita ba.

“Jami’an ƴan sanda na ci gaba da watsa zafafan kalamai a jaridu da soshiyal midiya masu iya harzuka ƴan sanda a kan sojoji.

Burgediya Omoigui ne ya sawa sanarwar hannu a madadin Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai.

“Don haka kwamandoji su tabbatar su na wayar wa sojojin da ke karkashin su kai cewa su yi hattara da kaffa-kaffa wajen mu’amala da ƴan sanda, bayan wannan kisa da aka yi.”

Sanarwar ta ma kara da cewa sojoji su guji karakaina a cikin kakin soja, sai fa idan ta kama dole.

Kakakin Yada Labarai na ƴan Sanda na Kasa, Frank Mba, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba zai iya cewa komai ba, domin ba a aiko masa da wadannan shawarwari da mahukuntan sojoji suka yi wa jami’an sojoji ba.

Share.

game da Author