KARANCIN KUDADEN SHIGA: Buhari ya rubuta wa Shugaban tara haraji wasikar damuwa

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida wasikar nuna damuwa dangane da tabarbarewa da karancin kudaden shiga a aljihun gwamnatin tarayya tun daga 2015 zuwa 2018.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES a yau Lahadi cewa wasikar wadda tuni ta karade shafukan soshiyal midiya, an rubuta wa Babatunde Fowler ita ce tun a ranar 8 Ga Agusta.

Ta na dauke da sa hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari. Ta na dauke da bayanai da tambayoyi kamar haka:

“An fahimci cewa ana samun daburtaccen kiyasi da kuma adadin kudaden harajin da ake tarawa tun daga shekarar 2015 har zuwa 2018. Wannan daburtattun adadin kudade sun kunshi na dukkan abin da ake yanka wa haraji na wadannan shekaru uku.”

An dai nada Fowler shugabancin Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS) cikin 2015. Ya canji Samuel Odugbesan, wanda tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya nada.

Kafin nada shi na kasa, Fowler ya rike Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Lagos, jihar da ta fi dukkan sauran jihohin kasar nan karfin arziki.

Nazari da bitar kudaden da Hukumar Tara Haraji ke tarawa a shekara kafin hawan Buhari da Fowler a 2015, ya nuna cewa a shekarar 2006 ce kadai FIRS ta kasa tara harajin da ta yi kiyasin samu a kasafin kudin ta.

Amma kuma wasikar nuna damuwar da aka aika wa Fowler daga Fadar Shugaban Kasa, ta yi bayanin shekarun 2012 da kuma 2014 kadai.

“Mun kuma fahimci cewa kudaden harajin da Hukumar FIRS ta tara a shekarar 2015 da 2017 ko kadan ba su ma kai na 2012 da 2014 ba.”

Haka wasikar wadda Abba Kyari ya sa wa hannu ta kara tuhumar Fowler.

“Don haka ana gayyatar ka da ka zo Fadar Shugaban Kasa ta yi bayanin dalilin da ya sa ba a samun kudaden shiga kamar yadda ya kamata a ce ana tarawa.”

A ranar Litinin 19 Ga Agusta ne aka umarci Fowler ya je ya yi bayani.

PREMIUM TIMES ta kasa samun Kakakin Yada Labarai na Hukumar FIRS, Wahab Gbadamosi. Da ta tsananta neman sa, sai wata kwakwarar majiya ta ce ya tafi kasar waje.

PREMIUM TIMES ta ji cewa Fowler da manyan jami’an da ke karkashin sa na ta hakilon ganin sun zauna tsaf sun rubuta wa Fadar Shugaban Kasa gamsasshen bayani.

Idan ba a manta ba, Najeriya ta afka cikin halin matsin tattalin arziki bayan hawan Buhari mulki ba da dadewa ba.

Fowler ya hau shugabancin FIRS a daidai lokacin da Najeriya ke cikin halin kaka-ni-ka-yi.

An aika wa Fowler wannan wasika ce bayan EFCC ta damke wasu manyan mukarraban sa da aka zarga da yin sama-da-fadin bilyoyin kudade.

Share.

game da Author