KANJAMAU: Najeriya ta samu tallafin Dala miliyan 75 daga PEPFAR

0

Asusun yaki da kawar da Kanjamau na kasar Amurka (PEPFAR) ya bayyana cewa zai kara tallafawa Najeriya da dala miliyan 75 domin kawar da cutar a kasar.

Jakadan kasar Amurka Stuart Symington ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a cikin wannan mako a Abuja.

Symington ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta yarda ta kara bada wannan tallafi ne bisa ga kokarin da ta gani cewa Najeriya na yi domin kawo karshen yaduwar cutar a kasar da kuma wadata masu fama da cutar da magani akai-akai.

Sai dai kumu duk da haka yace sai gwamnatin Amurka ta gamsu da adadin yawan kudaden da gwamnatocin tarayya da jiha ke warewa domin kula da masu fama da cutar da ingancin kulan da suke samu a asibitocin kasar kafin ta saku kudaden.

Shugaban kula da kiwon lafiyar jama’a na asusun PEPFAR Mahesh Swaminathan ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa asusun ta kashe dala biliyan 4.7 a tsakain shekaru 14 wajen tallafa wa Najeriya don a kawar da kanjamau a kasar.

Swaminathan ya ce binciken da hukumar hana yaduwar cutar kanjamau (NACA) ta gudanar ya nuna cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar a Najeriya.

Binciken ya kuma nuna cewa mutane miliyan 1.4 masu shekaru 15 zuwa 49 ne ke dauke da cutar inda a ciki kashi 1.9 mata sannan 0.9 maza ne.

A jihohi kuma jihar Akwa Ibom ce ta fi yawan mutanen dake fama da cutar inda adadin yawan mutanen sun kai kashi 5.5 sannan jihar Benuweh dake biye mata na da kashi 5.3.

Shiyyar kudu maso kudu ne ya fi yawan adadin mutanen dake fama da cutar.

Ya ce a dalilin haka asusun ya fara shirin samar da magunguna wa mutane 180,000 a jihar Ribas.

Share.

game da Author