A ranar Talata ne kotu a Kaduna ta umurci wata matar aure mai suna Hauwa’u Zailani ta dawowa tsohon mijinta Akilu Yakubu da Katifarsa da Ledan daki da tafi dfasu bayan ya sake ta.
Alkalin kotun Muhammed Shehu- Adamu ya yanke wannan hukunci ne bayan raba auren Hauwa’u Zailani da Yakubu da yayi.
“Daga yau auren Hauwa’u da Yakubu ya Kare, na raba shi saidai kuma ya umarci Hauwa’u ta maido wa Yakubu, wato tsohon mijinta da katifar sa da Ledan daki da ya siya mata.
Hauwa’u dake zama a kauyen Gardanko a jihar Kaduna ta bayyana cewa tun bayan auren su Yakubu bai sake tanka ta ba.
“Na bar gidan Yakubu ina dauke da karamin ciki sannan a tsakanin wata takwas din da na yi a gidan iyayena, na rika fama da rashin lafiya da ya sa na yi barin wannan ciki. Duk tsawon wannan lokacin da na yi Yakubu bai taba lekowa ya ji halin da nake ba.
Saidai kuma Yakubu dake mazaunin kauyen Kabobo ned ya musanta korafin da Hauwa’u ta shigar gaban kotu, ya ce Hauwa’u ta koma gidan iyayenta ne domin ta nemi maganin rashin lafiya da take fama da shi.
Ya roki kotu da ta kara bashi lokaci domin ya ya sasanta da matarsa cewa har yanxu yana sonta.