Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya umarci duka hakiman dake jihar Kano da su bi sabbin sarakunan da suke ƙarƙashin su ba na Kano ba.
Darektan yaɗa labaran gwamna Ganduje Abba Anwar ne ya fitar da wannan sanarwa a madadin gwamnan.
Sanarwan ta gargaɗi dukka hakimai da su tsaya a masarautun su domin yin hawan Sallah.
” Gwamnatin Kano ta ƙaryata raɗe-radin da ake ta yadawa wai ta umarci hakimai su garzayo masarautar Kano domin yin hawan Daushe.
” Gwamnatin Kano bata da masaniya game da wannan sanarwa kuma ba daga gareta ya fito ba. Sakon gwamnati shine kowani hakimi ya yi hawa tare da sarkin kasarsa.
” Hakiman dake ƙarkashin Bichi, za su yi hawa tare da sarkin Bichi ne, Hakiman Ƙaraye, suma da nasu sarkin da dai duka sauran hakiman masarautun da aka ƙirƙiro.
” Kada wani hakimi ya kuskura ya bi wani sarkin da ba a ƙarƙashin shi ya ke ba. Na Kano su bi na Kano haka sauran.
Hakimai da dama a jihar Kano sun ci gaba da yi wa sarkin Kano Sanusi ne mubaya a duk da sabbin manyan masarautu da gwamna Ganduje ya ƙirƙiro.
A ranar Asabar ne wato jajibarin Sallah ,Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulƙadir ya dakatar da Hakimin Wudil Sarki Ibrahim, Hakimin Gabasawa Bello Abubakar, Hakimin Warawa, Kabiru Hashim, Hakimin Dawakin Kudu, Yusuf Bayero da Hakimin Garko Mohammed Aliyu domin sun ƙi yi masa biyayya.
Discussion about this post