Jariri 1 cikin jarirai 3 ne ke samun shayarwar nono zalla na tsawon watanni 6 a Najeriya – Bincike

0

Sakamakon bincike da aka yi a Najeriya ya nuna cewa jariri daya ne tal cikin jarirai uku ke samun shayarwar nonon uwa zalla na tsawon watanni shida a Najeriya.

Cibiyar kula da kiwon lafiyar mata ta kasa ce ta gudanar da wannan binciken sannan ta gabatar da sakamakon haka a taron wayar da kan mutane mahimmancin shayar da ‘ya’yan su nonon uwa da aka yi a Abuja a wannan mako.

A taron, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga duka sassan gwamnati kan kirkiro dokokin da zai taimaka wajen inganta shayar da jarirai nonon uwa zalla musamman na tsawon watanni shida.

Ta ce samar da doka irin haka ya zama dole ganin cewa shayar da jariri nonon uwa na samar masa kariya daga kamuwa daga cututtuka da kuma kare shi daga yunwa.

Bayan haka binciken da cibiyar NNHS ta gudanar a 2018 ya nuna cewa har yanzu Najeriya na kashin baya wajen shayar da jarirai nonon uwa.

Binciken ya nuna cewa kashi 27 bisa 100 na jarirai ne kawai a kasar nan ake shayar da su nonon uwa zalla na watanni shida.

Pernile Ironside na Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta bayyana cewa shayar da jariri nonon uwa zalla na tsawon watanni shida sannan na tsawon shekaru biyu dabara ce dake samar wa yaro kariya daga cututtukan dake yin ajalin jaririn kafin ma ya kai shekara 5.

Ironside ta ce kamata ya yi a ware shekara daya domin wayar da kan mutane mahimmancin samar wa ‘ya’yan su irin wannan kariya.

Ta kuma ce gwamnati za ta iya bai wa mata da maza hutu da zaran mace ta haihu domin inganta shayar da jariri nonon uwa.

Sannan gwamnati ta kafa dokar da zai taimaka wajen rage siyar da abincin da za a iya ba jariri.

Darektan fannin kiwon lafiyar iyali a ma’aikatar kiwon lafiya Adebimpe Adebiyi ta ce shayar da jariri nonon uwa zai taimaka wajen rage yawan mace manen yara kanana a kasan nan.

Ta ce bincike ya nuna cewa yara 800,000 ne ke mutuwa a duniya duk shekara a dalilin rashin shayar da su nonon uwa sannan hakan yafi muni a Najeriya.

Share.

game da Author