Hukumar kula da gidajen Radiyo da Talabijin ta kasa (NBC) ta amice wa jami’ar Bayero dake Kano ta bude gidan Talabijin din kanta domin koyar da dalibanta dake koyan aikin jarida a jami’ar.
Shugaban hukumar Ishaq Kawu ya sanar da haka ranar Talata a lokacin da yake amsar bakuntar mahukunta daga jami’ar da suka kai masa ziyara a ofishin sa dake Abuja.
Kawu ya ce hukumar ta baiwa jami’ar Bayero lasisin yin haka ne a bisa kyakkyawar alaka da zumunta dake tsakanin hukumar da jami’ar musamman sashen koyar aikin Jarida na jami’ar.
“ Yanzu dai jami’ar Bayero ta samu lasisin bude gidan talabijin din kanta domin koyar da dalibanta yadda ake aikin jarida musamman wadda ya shafi aikin talabijin da Radio.
Dama dai jami’ar Bayero ta na da gidan Radiyo na kanta da take watsa labarai a jami’ar da wasu sassan Kano.
A jawabinsa shugaban jami’ar Farfesa Muhammed Bello ya mika godiyarsa ga Kawu da hukumar NBC bisa wannan goma ta arziki da hukumar ta yi wa jami’ar.
Bello yace lallai jami’ar za ta yi amfani da wannan dama domin koyar da daliban jami’ar dabarun aikin talabijin da kuma watsa shirye-shirye domin daliban, jami’ar da mutanen jihar Kano baki daya.
Rajistaran jami’ar Binta Mohammed da shugaban Sashen karatun gaba da digiri na jami’ar Umar Pate na daga cikin tawagar da suka kai wa hukumar ziyara.