Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai miƙa saƙon gaisuwar Barka da Salla ga ilahirin mutanen jihar Kaduna da sauran mulumai baki ɗaya.
El-Rufai ya yi kira ga mutanen Kaduna da suyi koyi da karantarwar Annabin rahama SAW musamman a wannan lokaci na babbar sallah.
Sannan kuma miƙa gaisuwar Sallah ga Alhazawan mu ƴan jihar Kaduna dake ƙasar Saudi.
A tawagar gwamna El-Rufai a filin idi, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna, Mohammed Abdullahi, sakataren gwamnatin jiha, da kwamishinan matasa na jihar, Farfesa Kabiru Mato.
Discussion about this post