HAJJIN BANA: Alhazai 313 sun rabu da ‘Taba Sigari’ kwata-kwata – Kaffa

0

Shugaban gidauniyar ‘Kafa’ da ke aikin taimaka wa Alhazai wajen kiwon lafiyar su ta ce a bana akalla Alhazai 313 ne suka rabu da taba sigari kwata-kwata.

Abdullah bin Dawwod Al-Fayez da ya bayyana haka ya ce wannan aiki da suke yi ya taimaka wa Alhazai da dama musamman a Muna, inda da yawa suka garzayo asibitin su domin neman magani.

Ya ce wannan shiri ne tare da hadin guiwar gwamnatin kasar Saudiyya, ma’aikatar kiwon lafiya na Saudiyya da kuma kungiyar ‘Ghazaleh charity’.

Asibitin Kafa da ke aiki a Makka, ya duba marasa lafiya fiye da 100,000 a bana.

Share.

game da Author