Jagoran fannin dake kula da kiwon lafiyan Alhazai na hukumar NAHCON Ibrahim Kana ya bayyana cewa adadin yawan alhazan Najeriya da suka rasu a Saudi a Hajjin bana ya kai akalla mutane Tara.
Kana ya fadi haka ne da yake ganawa da manema labarai a Muna.
Ya ce daga cikin mutanen da suka rasu akwai wata mata daga jihar Legas wacce sai da ta suma ranga-ranga a Jamrat.
“ Hajiyan ta rasu bayan an kawo ta asibiti a Muna sannan a wannan lokaci ne muka gane cewa ashe hawan jinin ta ne ya tashi inda ya yi bugu daya.
Daga nan Amir din jihar Legas Abdulateef Abdulkarim ya fadi sunnan matar da ta rasu a Jamrat.
Abdulkarim yace sunan matar Folashade Lawal daga karamar hukumar Oshodi kuna ta rasu ne da misalin karfe uku na Asuba a wajen jifan shaidan.
Bayan haka Kana yace sun bude kananan asibitoci guda 21 a Muna domin kula da Alhazan Najeriya.
“Asibitocin namu na dauke da isassun magunguna, kwararrun ma’aikata da motocin daukan marasa lafiya kuma”.
Ya ce hawan jini,mura da tari ne cututtukan da Alhazan Najeriya suka fi fama da a Hajjin bana.
A yanzu dai Alhazan Najeriya na ta siye-siyen kayan tsaraba domin iyalai da abokan arziki inda wasu kuma suna kikarin kammala aikin hajjin su ne.
A karshe wata majiya ta bayyana cewa NAHCON ta tsayar da ranar 17 ga watan Agusta a matsayin ranar fara dawo da Alhazan Najeriya.