Gwamnatin jihar Yobe ta saka hannu a takardar yarjejeniyya da kamfanin ‘Family Home Fund (FHF) Ltd’ domin gina gidaje 2600 wa mutanen jihar.
A lissafe dai gwamnati zata bukaci Naira biliyan 10.8 domin gina wadannan gidaje a shiyoyi uku dake jihar sannan za a kammala ginin wadannan gidaje ne a cikin watannin 18.
A jawabin sa gwamnan jihar Mai-Mala Buni ya bayyana cewa gwamnati ta yi haka ne domin samar da gidajen zama ga mutanen ta domin ci gaban su.
“Za mu gida wadannan gidaje a shiyoyin dake Yobe da Damaturu. A shiyar A dake Yobe za a gina gidaje 500,a shiyar B gidaje 300, a shiyar C gidaje 250 sannan a Damaturu za mu gina gidaje 1000.
Gwamna Buni yace za a yi bukin aza tubalin ginin wadannan gidaje ne a ranar bukin cikan wannan gwamnati kwanaki 100.
A karshe shugaban kamfanin FHF Femi Adewole ya bayyana cewa kamfanin zata samarda tallafi na kudade da kayan aikin da za ta bukata domin ganin an gina wadannan gidaje cikin ingancin kuma akan lokaci kamar yadda gwamnati ta shaida.
Daga nan sai yace gwamnatin jihar Yobe za ta biya bashin wadannan kudade ne cikin shekaru 10 masu zuwa.