A karkashin shirin ciyar da yara ‘yan firamare da gwamnatin tarayya ta bullo da shi an samar da kwanukan tasa da cokullan cin abinci ga yara da ke firamare su 13,482 a Jihar Jigawa a Karkashin Shirin Ciyar da Dalibai Abinci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Kodinatan shirin SIP na yankin mai suna Shehu Baba, shi ne ya damka kayayyakin ga masu dafa abinci 149 na Karamar Hukumar Birniwa.
Da ya ke magana a wurin raba kayan, Baba ya ce za a ajiye kwanukan da cokullan a wajen shugabannin da ke dafa abinci domin a rika cin amfanin su ta yadda ya dace.
Ya kara da cewa an samar da wannan tsari a makarantu 106 na yankin.
Baba ya kara yin bayanin cewa gwamnatin tarayya ta samar da kwano da cokullan domin ‘yan makaranta su rika cin abinci a cikin wari mai tsafta.
Daga nan sai ya umarci dukkan hedimastoci su kai masa rahoton duk uwar-tuwon da ta zaba wa yara abinci a cikin kwano maras tsafta.
Ya kuma hori hadimastoci da masu aikin dafa abinci, da su kara jaddada wa dalibai muhimmamcin kula da kwanuka da kuma tsaftar su.
Shirin ciyar da dalibai na daya daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fito da shi domin rage wa masu karafin karfi radadin kuncin rayuwa.
Discussion about this post