Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da yi wa jama’a aiki wurjanjan, kuma ayyukan da za su bai wa jama’a mamaki kwaran gaske.
Buhari ya yi wannan bayani ne a yau Alhamis, lokacin da ya ke bude Aikin Fadada Samar da Ruwan Sha a Zariya, jihar Kaduna.
Ya ci gaba a cewa duk da karancin kudi da gwamnatin sa ke fama da su, ta kashe naira bilyan 11.8 gina madatsar ruwa mai cin cibic meters milyan 186.1 a Galma.
“Wannan aiki ne hadin guiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihar Kaduna da kuma Bankin Musulunci na Afrika.
Buhari ya kuma jinjina wa Gwamna Nasir El-Rufai saboda yadda ya kammala aikin ruwan, wanda ya shafe shekara da shekaru a baya ba a kammala ba.
Sannan kuma ya gode wa Jihar Kaduna ganin yadda jihar ke maida hankali wajen gudanar da ayyukan ci gaban al’umma.
“Shi ma Bankin Musulunci na Afrika ya yi rawar gani sosai wajen bada hadin kan samar da kayayyakin aikin wannan ruwa na Zariya.
Buhari ya ce da taimakon bankin matuka gaya aka samu nasar kammala aikin.
Daga nan sai ya kalubalanci Hukumar Samar Da Ruwa ta Jihar Kaduna da su kula sosai da aikin ruwan kuma ya yi kira ga al’ummar yanki da su kula da kayan sosai, tare da biyan kudin ruwan da za su rika sha.
Buhari ya ce da kudin bashi aka gida wurin samar da ruwan, kuma za a dade shekaru masu yawan gaske, kafin a kammala biyan bashin.