Gwamnati na za ta fitar da talakawa milyan 100 daga cikin fatara da talauci –Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta shirya tsare-tsare yadda za ta fitar damatasa milyan 100 daga kangin talauci.

Buhari ya ce nan da 2023 ne gwamnatin ta sa za ta cimma samun nasarar wannan kuduri da ya ce gwamnatin sa ta dauka, kuma ta ke da shirin aiwatarwa.

“Wannan nasara tabbas za ta dora Najeriya a sahun farko na “Kasaitattun Kasashen Duniya.”

Buhari ya yi wannan albishir ne a lokacin da ya ke jawabin bude taron sanin makamar aiki da aka shirya wa sabbin ministoci a Abuja.

Shugaba Buhari ya yi Kungiyar World Poverty Watch ta ce a duk shekara rashin aiki yi a hannun matasa sai kara muni ya ke yi.

MASU MAKAUNIYAR ADAWA NE BA SU GANIN KOKARIN DA AKA YI WAJEN DAKILE RASHAWA DA KAWO TSARO

Buhari ya kuma jaddada irin kokarin da gwamnatin sa ya ce ya yi wajen magance tsaro, tattalin arziki da dakile cin hanci da rashawa.

“Masu makauniyar adawa ce kadai ba za su ga kokarin da aka yi a fanni tsaro da kuma dakile cin hanci da rashawa.” Inji Buhari.

Ga Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari Nan Dalla-Dalla:

1 – Ina yi muku barka da zuwa wurin wannan kasaitaccen taro, wanda dalilin gudanar da shi, don a sanar da ku irin nauye-nauye da kalubaken da ke gaban ku. Domin za mu yi aiki tare na tsawon shekaru hudu da yardar Allah Madaukakin Sarki.

2. Ina kuma yi wa dukkan sabbin shigowa majalisar dattawa barka da shiga, saboda kasar ku ta zabe ku a matsayin ministoci, duk kuwa da cewa akwai dimbin jama’a da ba su samu wannan damar ba.

An zabe ku ne domin ku taya Shugaban Kasa tafiyar da mulkin kasar nan.

3. abin alfahari ne kwarai a gare ku cewa an kira ku domin ku taya ofishin shugaban kasa mai alfarma aiki. Don haka akwai aiki tukuru a gaban ku. Sai ku zage damtse sosai domin cimma wannan buri da ke gaban mu.

4. Na san kuma duk mu na sane da cewa yawan mu ya kai milyan 200, a kididdigar game-gari. Nan da shekarar 2050 za mu kai milyan 411, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasi, hasashe da kuma kisdado. Kenan zuwa wancan lokacin za mu kasance kasa ta uku wajen yawan Al’umma da kakaf duniya, bayan Chana da Inidiya.

5. Wannan abu ne mai jefa mana fargaba, amma fa har sai idan mun dan zuna mu na jiran wasu abokan hulda hulda kasashe rokon su kawar mana da matsalolin na mu. Maganin mu ya na a wurin mu, ba a hannun wasu can ba.

6. Ya ku sabbin ministoci, a farkon hawan mu mulki, sun kebe wasu bangarori uku, na tsaro, tattalin arziki da kuma kawar da cin hanci da rashawa.

7. Babu wanda zai yi gardama ko tababar ko tantamar wannan nasara da muka samu ta inganta wadannan bangarori uku, sai fa masu adawa ido rufe kawai.

8. A matsayin kun a ministoci, ina yi maku kyakkyawar fatan cewa za ku hadu da masu bada shawarwari da masu taimakawa domin a gina kasaitacciyar Najeriya.

9. Yayin da wannan gwamnatin ta mu za ta cika shekaru takwas, za mu ceto mutane milyan 100 daga matsalar kuncin rayuwa da datara da talauci. A lokacin kuma Najeriya za ta kai kan ta a sahun gaba na kasaitattun kasashen duniya.

10. Ku ne za ku dauki alhakin bada iznin gudanar da ayyuka a karkashin ma’aikatun ku. Sannan kuma ku tabbatar hukumomin da ke karkashin ku na aiki tukuru kamar yadda aka tsara a kan ka’ida.

11. Ina jan hankalin ku da ku yi aiki kafada da kafada da juna, duk da dai kowa da bangaren da aka wakilta masa kulawa da shi.

13. Ku kasance kun dauki wannan taro da muke yi a matsayin wani fara shiri na kai Najeriya a Mataki na Gaba. Ina yi muku fatan alheri.

Share.

game da Author