Gwamnan Bauchi ya nada wanda Buhari ya kora Kwamishina

0

Daya daga cikin mutane 20 da Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya nada kwamishina, an taba samun sa dumu-dumu cikin harkalla da asarkalar yin amfani da mukamin sa na Shugaban Gidan Radiyon Tarayya, FRCN ya yi cuwa-cuwa da kumbiya-kumbiyar kudade.

Ba wani ba ne, sai Ladan Salihu, wanda a cikin 2016, Shugaba Muhammadu Buhari ya kore shi daga shugabancin FRCN, saboda samun sa da harkalla.

Shi ma gwamnan har zuwa ranar da aka rantsar da shi, ya na fuskantar tuhuma a kotu bisa zargin karkatar da makudan kudade a lokacin da ya na Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja.

An dakatar da shari’ar da ake tuhumar Bala ce, saboda an rantsar da shi Gwamnan Jihar Bauchi. A dokar Najeriya dai gwamna ya na da kariya, ba za a gurfanar da shi kotu ba, har sai bayan ya kammala wa’adin sa.

Bala ya mika sunayen kwamishinonin sa ga ‘yan majalisar da ake tafka kwatagwangwamar yadda aka yi zaben shugabannin su.

Ya mika sunayen ne ranar Alhamis da ta gabata.

Cikin wadanda ya mika sunayen na su, har da fitaccen dan soshiyal midiya, kuma masanin shari’a da dokokin kasa, Aminu Gamawa.

Gamawa ya yi Digirin-Digirgir a mashahuriyar Jami’ar Harvard. Kuma dama a can ya yi digirin sa na biyu, duk a kan sanin hukunce-hukuncen dokoki da aikin lauya.

Akwai kuma tsohon na hammnun daman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda tuni ta dawo daga rakiyar shugaban kasa din ya na sukar tafiyar tsarin mulkin sa a soshiyal midiya. Ba wani ba ne sai fitaccen mai rajin nan a Arewa, wato Aliyu Tilde.

Shi kuwa Ladan Salihu, bayan korar sa da Buhari ya yi daga FRCN a cikin 2016, sai ya nemi takarar zama sanatan Bauchi, amma bai yi nasara ba.

Daga nan kuma sai ya bi zugar siyasar Bala Mohammed, ya zama daraktan yada labarai na kamfen din Bala a takarar neman gwamnan jihar Bauchi. Sun yi nasara, guguwar Bala ta kayar da gwamana Mohammed Abubakar na APC a zaben 2019.

Sai dai kuma duk dac cewa an taba bada shawarar a kori Ladan Salihu daga FRCN, sai ma aka nada shi ya zama Babban Daraktan Gidan Radiyon na gwamnatin tarayya.

Cikin 2015 PREMIUM TIMES ta buga labarin duk yadda Salihu ya bi har ya zama shugaban FRCN.

Wasu kwafe-kwafen takardu da PREMIUM TIMES ta bi ta wasu hanyoyi ta samo, sun fallasa yadda aka kauce ka’ida aka dirka satar kudade.

Wannan barusa ce ta sa har aka rubuta wa Salihu takardar gargadi, kuma aka zabtare masa rabin albashin sa, aka rika biyan sa rabi kawai.

Kadan daga cikin barankyankyamar da aka kama Ladan Salihu da ita, it ace yadda a cikin 2009, aka same shi da hannu dumu-dumu wajen buga rasidin jabu, a lokacin da ya na Daraktan FRCN, Shiyyar Kaduna.

Wannan cuwa-cuwa ce ta sa ShugabanFRCN na lokacin, Yusuf Nuhu Nuhu ya zabtare masa albashi, aka rika biyann sa rabi kawai.

Sai dai kuma da mai juyawa ta yi wani juyin waina, sai aka wayi gari Salihu ne yah au kujerar shugabancin FRCN, bayan saukar Nuhu.

Akwai kuma wani labara can daban da PREMIUM TIMES ta taba bugawa, na yadda Salisu ya rika karkatar da kudaden gwamnati zuwa cikin asusun ajiyar sa na banki.

Sai dai kuma duk da wannan alamar tambaya da kamun da aka yi wa Salisu da korar sa da Buhari ya yi, wannan duk ba ta hana Majalisar Jihar Bauchi sun wanke shi ba, har an nada shi minista.

Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin Yada Labari na Gwamna Bala, ya ce daga shi har gwamnan babu wanda ke da masaniyar an taba kama Salihu dumu-dumu cikin badakalar kudade.

Share.

game da Author