Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Zamfara Lawal Liman ya gargadi ‘ya’yan jam’iyyar da kasa su saka baki akan binciken da ake yi wa tsohon gwamna jihar AbdulAziz Yari.
Hukumar EFCC da ICPC suna bincikar tsohon gwamna AbdulAziz Yari kan zargin wawurar kudin jihar a lokacin yana gwamnan jihar Zamfara.
Liman ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar na jihar da su kame bakinsu daga cewa komai game da wannan bincike har sai an kammala.
” Yari mutum ne mai bin doka da Oda saboda haka yana kiran yayan jam’iyyar dasu ci gaba da bin dokokin jam’iyyar.
Discussion about this post