FADUWAR GABA HASARAR NAMIJI: Ni zan yi nasara a kotun Daukaka Kara – Dino

0

Sanatan dake wakiltan Kogi ta yamma Dino Melaye ya bayyana cewa hukuncin Kotu da ta zartar wai sai an sake zaben kujerar sa na sanata bai dadasa da kasa ba ko kadan.

Dino yace dama can koda ace shine aka ce yayi nasara sai abokin hamayyar sa ya garzaya kotun daukaka kara.

” Ina kira ga daukacin magoya baya na da su kwantar da hankalinsu, nasara na tare da mu. Wannan hukunci bai dadani da kasa ba ko kadan kuma ko a koyun daukaka kara zamu yi nasara.”

” Sannan kuma ma ay ko ba don wannan hukunci ba dole sai an sake zabe na kujeran sanatan Kogi ta Yamma domin nine zan zamo gwamnan jihar Kogi.

Idan dai ba a manta ba kotu ta soke zaben sanata Dino Melaye da ke wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar Dattawa.

A hukuncin da kotun ta yanke wanda Sanata Smart Adeyemi ya shigar ta ce wannan zabe ba a yi shi cikin gaskiya ba wanda a dalilin haka sai an sake zaben.

Share.

game da Author