El-zakzaky ya shirga Ƙarya ne, shine ya ƙirƙiri wasu ɗabi’u a Indiya – Inji Gwamnati

0

Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata saƙon sautin da Sheikh Ibrahim El-zakzaky ya fitar daga ƙasar Indiya inda ya koka kan yadda aka hana shi sakat da matarsa Zenat a asibiti.

Idan ba a manta ba, El-zakzaky ya saki saƙon sauti da ke kunshe da bayanan yadda ake muzguna masa a asibiti a Indiya.

A martani da gwamnatin Najeriya ta yi game da wannan saƙo, Najeriya ta ce babu gaskiya a cikin duka abin da El-zakzaky ya faɗi.

Grace Gekpe, babban sakatariyar ma’aikatan Yaɗa Labarai da Al’adu ta ce tun a ƙasar Dubai kafin ma su isa Indiya, El-zakzaky ya fara nuna wasu halaye da ba haka a ka shirya da shi ba.

” Na farko dai ana isa filin jirgi a Dubai, sai El-zakzaky ya nemi jami’an dake tare dashi su miƙa masa Fasfo ɗinsa. Tun daga nan aka yi ta daga dashi har aka isa ƙasar Indiya.

” Sannan kuma ina so kowa ya sani cewa El-zakzaky da kansa ya zaɓi wannan asibiti da aka kaishi tare da mai daƙin sa.

” Bayan haka kuma sai ya ce shi ba zai kwanta a asibitin ba kuma a kama masa babban Otel ya koma can ya zauna sannan a janye ƴan sandan da ke tsare shi. Anan ne fa jami’ai suka ce Bisar sa ba na yawon shaƙatawa bane, saboda haka iyakan sa Asibiti.

” Sannan ya rika tilasta wa likitocin asibitin cewa ba za su duba shi ba sai dai an turo wasu zabaɓɓun likitoci da shi ya yarda da su su duba shi. Likitocin Indiya suka ce nan ko bai isa ba ko ya tsaya a duba shi ko kuma ya koma Najeriya.

Grace ta ci gaba da cewa haka fa aka yi ta fama da El-zakzaky har wakilan gwamnatin Indiya suka ce su fa baza su yarda ya shigo ƙasar su ya nemi ƙulla wata maƙarƙashiya ba, idan neman maganin ba zai yiwu ba toh fa gaskiya ya tattara ya koma Najeriya.

Share.

game da Author