El-Zakzaky ya isa asibitin Indiya

0

Tabbatattun bayanai sun nuna cewa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa Zeenat sun isa asibitin Indiya a yau Talata.

Sun bar filin jirgin Abuja jiya Litinin da yamma, inda suka yada zango, sannan suka karasa.

Wasu hotuna da Ibrahim Musa, Kakakin Yada Labarai na IMN ya buga a shafin sa na Facebook, ya nuna a kasan hotunan cewa jagoran na su da matar sa sun isa asibitin, tare da nuna yadda aka tarbe su.

Ganin jagoran mabiya Shi’a da matar sa sun samu kan su a asibitin Indiya, yanzu kuma abin da zai fi jan hankalin jama’a shi ne a ji takamaiman ciwon da ke damun sa, bayan rasa ido daya da ya yi da kuma lahani da hannun sa daya ya samu.

An nuno hoton malamin a filin jirgin Abuja daure da farin takunkumi a bakin sa, sannan wuyan sa ya na tallabe da da wani dauri.

TAFIYAR EL-ZAKZAKY: Yadda Buhari ya yi fatali da tsauraran ka’idojin El-Rufai

Hakan kuwa na nuni da cewa har yanzu malamin na fama da wasu lalurori da ke nuna ya na jin jiki.

Ita ma matar sa Zeenat, Kwamitin Fafutikar Neman Sakin El-Zakzaky da kuma lauyan su Femi Falana, sun tabbatar da cewa ta na fama da matsanciyar damuwa a cikin jikin ta.

Ko a jiya Litinin wata sanarwa da kwamitin ya bayar, ya tabbatar da cewa akwai tartsatsin albarusai a jikin Zeenat, wadanda tun bayan harbin da aka yi mata a ranar 15 Ga Disamba, lokacin da sojoji suka kai farmaki gidan ta, yau ba a kai ga cire mata ba.

Ko kwana nawa ko wata nawa marasa lafiyar za su iya yi, da kuma bayanan da za su fito daga bayanan su bayan sun samu lafiya, su ne duniya za ta zura ido ta jira a ji, kuma a gani.

Share.

game da Author