Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya aza tubalin gina manya-manyan shagunan zamani mai suna ‘Amsalco Galaxy Mall’ a jihar.
Za a kashe akalla naira Biliyan 3.9 a wannan aiki sannan za a kammala wannan iki cikin watanni 18.
El-Rufa’I yace gwamnati ta hada hannu da bankin UBA da kamfanin Amsalco domin gina shagunan kuma kamfani ‘CCECC Nigeria Limited’ ne za ta yi aikin.
” Gwamnatocin baya sun yi kokarin gina irin wannan kantuna amma bai yiwu ba. Wannan Karon zamu tabbatar an kammala wannan aiki. Mun samu hadin guiwar yan kasuwan jihar domin samun nasarar yin wannan aiki.
El- Rufai ya ce wannan aiki ne da jihar zata maida hankali wajen ganin ya kammalu kuma mutanen jihar sun mori shagunan.