EFCC ta kai farmaki gidan AbdulAziz Yari

0

Jami’an hukumar EFCC sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari dake Taƙatan Mafara, jihar Zamfara.

Kamar yadda rahotanni ya zo mana, jami’an EFCC ɗin sun diran ma gidan Yari ne ranar Lahadi.

Da yake tabbatar da wannan farmaki da aka kai gidan Yari Kakakin EFCC Tony Orilade ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa jami’an hukumar sun ziyarci gidan Yari a Zamfara kuma sun gudanar da bincike.

Idan ba a manta, Tabbatattun bayanai da ke a hannun PREMIUM TIMES sun tabbatar da yadda tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya bayar da kwangila daya sau biyu kuma ga mutum daya. Sannan kuma farashin kwangilar ya wuce-gona-da-iri.

Da farko an bayar da kwangilar gina rijiyoyin burtsatse 84 a fadin kananan hukumomi 14 na jihar a ga wani kamfanin kasar China mai suna China Zhonghao Nigeria Limited, a kan kudi naira bilyan 27.5. An bayar da kwangilar a cikin 2014.

Sai kuma aka dawo a cikin 2018 aka sake bayar da wannan kwangila kuma a kan wadancan adadin kudade, naira biliyan 27.5.

ZUKI-TA-MALLE: Babban abin tayar da hankali shi ne ita gwamnatin jihar a lokacin Yari, ta yi wa kwangilar kudi ne a kan gejin naira biliyan 19.7. Amma a ranar 3 Ga Oktoba, 2013, sai aka rubuta wa Manajan Darakta na kamfanin takardar amincewa da kwangilar a kan kudi naira bilyan 27.5. Wato an yi azuraren karin kusan naira biliyan 8 kenan, a bugun farko na kwangilar.

WALA-WALA: Yayin da aka zo wajen biyan kudi ga kamfanin, sai aka biya shi naira bilyan 19.3, maimakon naira bilyan 27.5 a cikin 2014.

Wannan bankaura ta faru ne a karkashin Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya. Sannan kuma tuni kwamitin da sabon gwamna Bello Matawalle ya kafa a karkashin tsohon mataimakin gwamna, Ibrahim Wakkala ya tabbatar da haka.

Wato dai Yari ya kara wa wannan kwangila zunzurutun kudi har naira bilyan 8.2 kenan.

Share.

game da Author