Duk da ni jigo ne a PDP Ina yaba wa Buhari da ƙirƙiro da shirin RUGA da yayi – Walid

0

Shugaban kwamitin amintattu na Jam’iyyar PDP, Walid Jibrin ya yi kira ga jihohin ƙasarnan da su rungumi shirin nan na sama wa Fulani makiyaya matsuguni na gwamnatin Tarayya, wato shirin RUGA.

Walid ya yi wannan kira ne da yake zantawa da manema labarai a garin Lafiya a lokacin shagulgulan babban sallah.

Walid ya ce wannan shiri na gwamnatin tarayya shiri ne da ya kamata kowa ya rungume shi domin samarda zaman lafiya a kasarnan.

” Ni ɗinnan ɗan jam’iyyar PDP ne, babu abin da ya haɗa ni da APC amma kuma idan abin ci gaba ya zo dole mu jinginar da bambamci na siyasa mu rungume shi, musamman idan ya shafi tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mutane.

” Duk jam’iyyar dake mulki a ƙasarnan muddun zata samar da ci gaba da tsara hanyoyi domin inganta rayukan mutanen ƙasa, toh lallai ina tare da wannan gwamnati. Ni siyasar ci gaba nake yi.

” Haka nake sannan a matsayina na Bafullatani, mun rungumi wannan shiri na RUGA da hannu bibbiyu domin amfanin ƙasa da mutanen mu Fulani. Wannan shiri zai samarwa Fulani, makarantu, asibitoci, gidajen zama da wuraren kiwo wanda shine Fulanin suka rasa.

” Aƙalla jihohi 12 ne suka rungumi wannan shiri harda jihar Nasarawa. Ina kira ga sauran jihohin ƙasarnan musamman wadanda suke kudu maso kudu da kudu maso yamma da su rungumi shirin hannu bibbiyu domin ci gaban ƙasa.

A ƙarshe Jibrin yayi ƙira ga Fulani da su kauce wa aikata ayyukan ta’addanci da ya haɗa da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran ayyukan alfasha.

Share.

game da Author