Dalilin da yasa Inyamirai suka lakada wa Ekweremadu dukan tsiya a Jamus

0

A ranar Asabar ne tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya sha dukan tsiya a wajen ‘yan uwan sa Inyamirai a kasar Jamus.

Ekweremadu ya ziyarci Jamus ne domin halartar taron ‘Yan kabilar Igbo mazauna kasar Jamus.

Isar Ekweremadu wannan wurin taro ke da wuya sai ‘Yan uwan sa Inyamirai suma haushi da ihu suna zagin sa.

Da yayi kokarin shiga dakin taron sai ko suka hau shi da duka suka jawo shi waje da karfin tsiya suka yaga masa riga.

Kamar yadda Ekweremadu ya fadi a shafinsa na Facebook, ya ce yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ne suka far masa a kasar Jamus.

” Na yi kokarin in yi musu bayani amma suka ci mini mutunci. Basu san irin kokarin da nayi bane wajen ganin shugaban IPOB Nnamdi Kanu, da sama masa beli.

Share.

game da Author