Rundunar ‘yan sandan tsaro na SSS ta bayyana wasu daga cikin dalilan da ya sa suka cafke shugaban kamfanin (Sahara Reporters) kuma dan takarar shugaban Kasa a a zaben 2019.
Idan ba a manta ba tun a ranar Asabar aka sanar da cafke Sowore bisa dalilin kokarin shirya gangamin na gudanar da zanga-zanfga a fadin kasar domin nuna gazawar gwamnati mai mulki wajen samar da tsaro da ababen more rayuga ga ‘yan Najeriya.
Kakakin runndunar Peter Afunanya, ya bayyana cewa hukumar ta gano cewa Sowore yana tattaunawa sannan da ganawa da wasu mutane a wasu kasashen waje domin wannan gangami da ya sa a gaba da hakan ya sa dole a taka masa burki domin kada ya kawo rudani a kasar nan.
Tuni dai har Sufeto janar din ‘yan sanda ya ba da sanarwar cewa kada wani ya fito domin wannan zanga-zanga da aka saka ranar litini 5 gawata ranar fara shi.
Adamu ya ce wannan zanga-zanga ya haramta.
Sai dai kuma kungiyoyi da dama da mutane suna ta tofa albarkacin bakinsu bisa wannan kame da aka yi wa Sowore, suna kira da a sako shi.
Har yanzu dai ba a kai shi kotu sannan ba a sake shi ba.
Masu Zanga- Zanga sun lashi takobin ci gaba da wannan zanga-zanga da ya kamata a fara shi ranar litini 5 ga watan Agusta.
Discussion about this post