Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya sake komawa mukamin sa na minista a Ma’aikatar Shari’a a zangon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari karo na biyu.
Ya bayyana cewa ya samu damar sake komawa a kan mukamin sa ne, saboda kokari da goyon bayan da ma’aikatan sa suka ba shi.
“ A kan haka na kara yin kira ku ci gaba da ba ni irin wannan goyon baya domin mu ciyar da kasar nan gaba.
Daga nan sai ya kara jaddada muradin sa na ganin ya kara samar wa ma’aikatan da ke karkashin sa samun tagomashin kulawa daga gwamnatin tarayya.
Ya gode wa ma’aikata ganin yadda suka tarbe shi hannu bi-biyu a cikin annashuwa a lokacin da ya shiga ma’aikatar jiya Laraba a matsayin Minista a karo na biyu.
Da ya ke magana, Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a, Dayo Akpata, ya jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda fikira da hangen nesan sa har ya sake nada Malami.
Ya ce sake nada Malami da Buhari ya yi, ya tabbatar da cewa shugaban kasar ya gamsu da irin rawa da kuma gudummawar da ya bayar cikin shekaru hudu na zangon sa na farko, har ta sa a yanzu aka sake zaben sa.
Daga nan sai shi ma ya yi kira ga ma’aikatan shari’a su mike tsaye wajen ci gaba da bai wa Malami wata sabuwar damar da ai sake samun nasara a aikin sa na fannin shari’a.
Malami ya yi kaurin suna a zangon sa na biyu wajen kare gwamnatin Buhari, a duk lokacin da aka zargi gwamnatin da danne hakkin masu rajin adawa da ita.
Ya kuma yi kaurin suna wajen kokarin kashe shari’ar wasu da ake kallon makusantan gwamnati ne, ta hanyar kwace shari’un su daga hannun EFCC zuwa ofishin sa.