Da gwamnonin Arewa irin Matawalle ne…, Daga Mohd Ibn Mohd

0

Rabon da ace an samu gwamna mai kishin mutanen sa a yankin Arewacin Najeriya, ya yi matukar dadewan gaske musamman tun dawowar dimokradiyya a 1999.

Za a iya cewa tun bayan gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da yayi abinda ba a taba tsammanin za a yi a jihar Kano ba sai ko yanzu da Matawallen Maradun Bello Mohammed yake yi a Zamfara.

A lokacin da Matawalle ya dare kujerar gwamnan jihar Zamfara, ya iske jihar cikin kamayamayar Siyasa, hare-hare da ta’addanci da kuma fitinar masu garkuwa da mutane.

A kullum sai kaji an kashe mutane, an yi garkuwa da mutane ko kuma an illata mutane a jihar.

Abin yayi tsanani da hatta garin Gusau babban birnin Zamfara ana mata kirarin shiga da alwalanka.

Jama’an jihar Zamfara sun rika yin tir da salon gwamnatin da ta wuce, wato gwamnatin AbdulAziz Yari da suke ganin bai maida hankali wajen kawo karshen wannan ta’addanci a jihar.

Masu sharhi suna cewa AbdulAziz Yari ya fi maida hankalinsa ga siyasa maimakon mutanen jihar.

” Tsohon gwamna Yari ya kaurace wa mutanen jihar, ya fi maida hankali ga siyasa da kuma zama a Abuja abin sa.

” Duk halin da jihar ta fada a wancan lokaci babu abinda ya fi maida hankali akai fiye da sheke ayarsa a Abuja kawai. Idan ka ganshi a Gusau sai dai idan ya shigo gyara siyasar sa.

Duk da cewa a wancan zango, jihar ke da ministan tsaron na kasa amma kuma abin kunya shine a karamar hukumar sa na Birnin Magaji ta’addanci ya fi zama abin tashin hankali.

Haka dai mutanen jihar Zamfara suka ci gaba da zama har Allah subhanahu wata’ala ya kawo gwamna Matawalle.

Babban abin da Bello Matawalle ya maida hankali a kai shine dawo da zaman lafiya da samar da tsaro a jihar.

Matawalle ya fara ne da shiga sako sako, kurdi-kurdi na jihar domin gano matsalar da ya kaiga jihar ta fada cikin wannan hali.

Cikin watanni uku da darewar sa mulki, da kansa ya karbo akalla mutane sama da 300 dake tsare a hannun masu garkuwa a fadin jihar. Sannan kuma ya fara zama ta musamman da mutanen da basa ga maciji fa juna da suka hada da Manoma, Makiyaya, ‘Yan banga da masu tada zaune tsaye a gari.

Ya rika zama da su yana tattauna dasu yana shiga tsakani domin ayi sulhu.

Baya ga haka duk a cikin watanni uku ya dawo da biyan ma’aikatan jihar da suka shafe shekaru ba a biyan su albashi. Sannan ya himmatu wajen diban matasa ayyuka babu kakkautawa.

A kullum gaka Matawalle kodai ya fito aiki ne ko kuma zashi aiki.

Wani abin burgewa da yabawa da gwamna Matawalle yayi a wannan Sallah shi gayyato Fulani Makiyaya da yayi ruga-ruga,tare da manoma duk aka jadu a filin wasa na Gusau tare da shi domin ayi bukin sallah.

Sannan kuma da kanshi ya shiga kasuwan dabbobi domin siyan ragunan Sallah cikin raha da mutunci.

Yanzu dai gwamna Matawalle ya zamo zakaran gwajin dafi a Arewacin Najeriya.

Mutane na cewa ina ma ace Matawalle ne gwamnansu a ko ina a fadin kasa.

Share.

game da Author