Cikakken Bayani kan Hukunce-Hukuncen laiya a Musulunci, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

Wannan ibada Sunnah ce ta wajibi akan mutanen kowane gida daga cikin gidajen musulmi. Allah ya umurce annabin sa Muhammad (SAW) da jama’ar wannan al’uma da suyi Layya, a cikin suratul kauthar Allah yace: (To, ka yi Sallah ga
ubangijinka kuma kayi yanka). Annabin rahama (SAW) ya yi Layya kuma ya umurci al’umarsa da su yi Layya.

Layya sunnar manyan annabawane, annabi Ibrahima (AS), yana da falala mai yawa, daga ciki akwai:

1. Babu awani aiki mai girman daraja ranar Sallah kamar Layya.

2. Ita ce aikin Ibadan da Allah yafi so ranar Sallah.

3. Daga kowane silin gashin dabbar Layya a kwai lada daya.

4. Yin Layya bin umurnin Allah ne, da nuna godia agareshi.

5. Yin Layya yana kusantar da bawa zuwa ga Allah (SWT).

6. Yin Layya raya sunar Annabawan Allah ne.

7. Yanada daga cikin hikimar Layya, akwai yalwatama iyalai, da kyautatawa talakawa da miskinai, a sakamakon kyauta da sadaqa da naman layyan.

Dabbar da ake layya da shi

Ana yin Layya da lafiyyar daba, wadda batada aibi ko kadan. Ba’a yin Layya da dabba mai ido daya, ko gurguwa, ko mai karyayyen kaho, ko mai gutsurarren kunni, ko busasshiya, ko ramammiya, ko kyamusassa, ko mai yankaken kunni, ko tsohuwar dabba, ko mai guntulallen bindi da sauran nakasu. Anfi so ayi Layya da lafiyya kuma kosashiyar dabbar da bata da aibu.

Ana yin Layya da dabba ‘yar shekara daya a cikin tumakai, Rago, ko tunkiya, sannan dabbar da ta shiga shekara ta biyu a cikin awakai, bunsuru ko akuya, sannan dabbar da ta shiga shekara ta uku a cikin jinsin shanu, sa ko saniya, sannan dabbar da ta shiga shekara ta biyar a cikin rakuma, rakumi ko taguwa. Amma mafi daraja she ne babban rago,
mai kaho, fari, mai baki a gefen idunsa, da kafafuwansa.

Mutane bakwai na iya yin Layya da rakumi daya ko sa daya. Su yi tarayya a cikin sa (wato su hada kudi, su siya rakuma ko saniya, su yi layyar da ita) Amma ba’a yin tarayya a cikin sauran dabbobin layya.

Lokacin Layya

Mai Layya zai yanka dabbar layyar sa ne bayan yankan limaminsa, idan an sakwo daga idi, ranar Sallah, idan hakan bai samuba, to, zai iya yin Layyarsa rana ta biyu ko ta uko bayan Idi, a kowane lokaci kafin
faduwar rana, a yini na uku bayan sallah.

Hukuncin mai Layya

1 – Daga daya ga watan Dhul-Hajj, mutumin da ke da niyyar Layya ba zai aske ko tsige gashin jikinsa ba, kuma ba zai cire wata fatan jikinsa ba, kuma ba zai yi yankan kumba, har sai ya yanka dabbar Layyar sa.

Wannan yana nuna cewa mai layya zai yi aski da yankan kumba da sauran tsaftar jiki, kafin daya ga watan shawwal.

Ana sa ran daya ga watan Dhul-Hajj na wannan shekara zai kama ranar Laraba, 23rd August, 2017.

2 – Ana son Mai Layya ya yanka dabbar sa da kansa, (macce ce ko na miji) bayan ya kwantar da ita a bankaren hagu ta fuskantar alkibla, sannan yace:“Bismillahi, Allahu Akbar, Allahumma Hadha minka wa laka, Allahumma hadhihi anni wa an ahli baiti” sannan sai ya yanka dabbar.

3 – Babu laifi wanda ba zai iya yankawa ba, ya wakilta wani ya yankamasa. Mace za ta yanka dabbar layyar ta da kanta, matukar tanada karfin halin yin yankan.

4 – Mai layya ya tsarkake zuciyar sa da ibadar layyar sa (wato ikhlasi don Allah) kuma ya wasa wukarsa kafin yanka layyar sa, sannan ya bude bakinsa (daga kamun bakin da yayi a ranar) da mafi soyuwan naman layyar sa, ana son yaci, ya yi sadaqa kuma ya yi kyauta.

5 – Mai Layya zai yanka dabbar layyar sa amamadin kansa, da iyalansa matattu ko rayayyu, kuma duk sunada cikkaken ladan Layyar. Kuma zai iya yiwa iyayensa matattu layyar ta kansu da nufin Allah ya kai ladan
agare su.

6 – Ya halatta mai layya ya ci bashin kudi don siyan dabbar layyar ko kuma ya ci bashin dabbar don yin layya, matukar ya nada halin biya cikin sauki ba tare da wata matsalaba, kuma yanada inda zai karbi bashin.

7 – Babu Laifi aba wanda ba musulmi ba sadqar naman layya ko kyauta,shin mutuminan kafiri ne ko kirista ne, koma wane iri ne shi, ana iya bashi kyauta ko sadaqar naman layya. (Sheikh Ibn Baz da Uthaimin).

8 – Haramun ne ga mai Layya ya siyar da wani abu a cikin dabban layyar sa, koda kuwa shi baya da bukatar wannan abun.

Kuma haramun ne mai layya ya biya mai fida da fata ko naman layya. Mai layya wajibinsa ne ya biya dukk wata dawainiyar gyaran layyar sa da dukiyar sa.

Allah kabamu ikon batamaka yadda ka shar’anta, kuma ka barba ibadun mu, ka yarda da ayyukanmu. Amin

Share.

game da Author