Wani kwararren likita ya bayyana cewa ba gaskiya bane cewa da ake yi wai duk macen da ta ke shayarwa bata jin dadin saduwa da mijinta sannan kuma ma wai yana kawo matsala wajen shayar da jariri.
Likitan ya ce ba gaskiya bane kuma cewa da ake yi wai maniyyin namiji na gurbata ruwan nonon da jariri zai sha.
” Camfi ne ake yi wai idan mace na shayarwa bai kamata ta sadu da mijin ta ba saboda wai maniyyi yana bata ruwan nono.”
” Babu wani dangantake da ke tsakanin maniyyi da ruwan nono, hanyar jirgi da bam, na mota da bam. Mace mai shayarwa zata iya saduwa da mijinta a kowani lokaci da take so a lokacin da take shayarwa. Sannan baya sa jariri ya kamu da ciwo.”
” Abinda nake so in sanar muku shine ku sani babu ruwan maniyyin namiji da ruwan nonon mace mai shayarwa. Wasu su kan rika cewa wai maniyyin namiji na gurbata ruwan nono. Wannan ba gaskiya bane.
Hanyar jirgi da bam, na mota da bam. Sannan mace zata ji dadin mijin a kowacce lokaci ta so a lokacin da take shayarwa.
Discussion about this post