N-power shine mafi girman tsarin gwamnatin Buhari na samar da abun yi ga matasan Najeriya wadanda suka dade a cikin fatara da talauci bayan kammala karatun digiri ko HND.
Bayan samun nasarar shugaba Buhari a karo na farko, yayi kokari matuka don ganin ya cika alkawarin da ya daukarwa matasa a lokacin yakin neman zabe.
A kokarin tabbatar da hakan ne yasa ya kirkiro N-power a karkashin shirin da ake kiransa da turanci ‘social investment programmes’.
Da farko, tsarin ya fara ne da matasa dubu dari biyu (200,000) a matsayin rukuni na farko (Batch A), sannan daga baya aka dauki matasa dubu dari uku (300,000) a rukuni na biyu (Batch B).
Wadannan matasa zasu yi aikin wucin-gadi na shekara biyu-biyu ne kacal suna kar6ar dubu talatin (30,000) a duk wata.

Wa’adin ‘yan rukuni na farko (Batch A) ya kare tun watan Disamba 2018, amma saboda rokon da mutane suke yi na bayyana tasirin tsarin ga dubu daruruwan matasan da suke cikinsa, yasa aka samar da ‘enhancement’ ga wadannan matasa.
Watan Agustan (August) da ya shige shine lokacin da ‘yan rukuni na biyu (Batch B) suka cika shekara daya a cikin tsarin. Ya zama saura shekara daya ya rage musu kamar yadda dokar tsarin take.
Tabbas a cikin mulkin Buhari a karkashin jam’iyar APC babu abun da yafi tsarin Npower bayyana tasirin gwamnati ga rayuwar ‘ya’yan talakawa. Akwai ‘transparency da accountability’ a cikin tsarin.
Tasirin da tsarin yayi a Najeriya ne yasa mutane suke bayar da shawarar mayar da matasan da suke cikin shirin ‘yan sandan alqarya (Community police) saboda a inganta tsaro a kasa. Ni ban san kasar da take kan tsarin gwamnatin tarayya (fedaraliya) da take da yan sandan gwamnatin tarayya kawai ba.
Wannan tunani ne mai kyau, kuma idan aka yi hakan, idan Allah yaso za a ga tasirin abun. Anyi kusan irin wannan tsarin a Rwanda, anyi amfani da ‘community policing’ lokacin ‘genocide’. Yin amfani da mutanen cikin alkarya (Gacaca) yayi tasirin gaske wajen kawo karshen rikicin.
Matasan zasu taimaka matuka wajen magance matsalar tsaro a yankunansu duba da yadda da yawa daga cikin matasan suna da ilimi da kuma sanin matsalolin da kasarsu take ciki.
Muna fatan duk wanda yake da ruwa-da-tsaki a gwamnati zai goyi bayan wannan cigaba saboda duk sanda aka samu tsaro a karamar hukuma za a samu a jiha. Hakazalika idan aka samu tsaro a jiha za a samu a gwamnatin tarayya.
Tabbas, Yin amfani da wadanda suke cikin Npower da NYSC zai fi sauki fiye da daukar sababbin ma’aikatan tsaro tunda komai na matasan (profile) ana dashi akan tsari (Data base).
Muna cikin farin ciki matuka don matasanmu zasu samu aikin yi na din-din-din, kuma za a rage cunkoso a kasuwar aikin yi (Labour market) saboda idan gwamnati ta sallami matasan da suke cikin tsarin, tabbas sune zasu koma su sake cinkushe kasuwar aiki kuma masu rauni daga ciki zasu zama masu karya doka.
Gaskiya, zamu jinjinawa gwamnatin Buhari idan ta tabbatar da wannan tsarin. Lallai jam’iyar APC zata kafa tarihin da ba a ta6a kafa wa ba a Najeriya.
Sannan za a samu ingancin tsaro insha Allah saboda kowane matashi zai zama mai kula da tsaron yankinsa. Wannan abu ne na hankali.
Allah ya shiryar damu.