Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Babban Bankin Tarayya (CBN) ya daina bayar da canjin kudaden waje ga masu fita su na odar kayan abinci.
Buhari ya bada sanarwar cire wannan sasauci ne a lokacin da ya ke wa Gwamnonin Arewa jawabi, lokacin da suka kai masa ziyarar Barka-da-Sallah a Daura inda ya ke hutun Sallah.
Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya fitar da wannan sanarwar a jiya.
Shehu ya ce Shugaba Buhari ya umarci Shugaban CBN, Godwin Emefile cewa:
“Daga yau ka da ka sake ka kara bada canjin kudaden kasashen waje ko da na sisin-kwabo ga masu fita waje su na safarar kayan abinci su na shigowa da shi kasar nan.”
“Mun samu nasarar iya noma abincin da za su iya ci kasar nan a wadace.”
Ya ci gaba da shaida musu cewa asusun rarar kudaden Najeriya da ke waje za a rika tassrifin su a wasu hanyoyin inganta tattalin arzikin kasa da kuma fadada wasu hanyoyin ci gaba kasa. Amma an daina karkata kudade wajen shigo da kayan abinci daga kasashen waje.
“Don haka mun kai gacin iya ciyar da kan mu da kuma dogaro da kayan abincin mu.
“Kada CBN ya kara bada canjin kudin kasashen waje ko na sisin-kwabo ga masu sayo kayan abinci su na shigo da shi a Najeriya.” Inji Buhari.
Buhari ya yi tsokacin cewa wasu jihohi irin su Kebbi, Ogun Lagos, Jigawa, Ebonyi da Kano tuni sun dauki shirin Gwamnatin Tarayya a kan inganta harkar noma hannu bib-biyu kuma su na cin moriyar albarka da ribar da ke tattare da shirin.
Daga nan sai ya yi kira ga sauran jihohi su tsunduma ka’in-da-na’in wajen bai wa shirin Wadata Najeriya Da Abinci muhimmanci.
Ya nuna farin cikin ganin yadda matasa ciki har da dimbin wadanda suka kammala digirin farko su ka tsunduma harkar noma gadan-gadan tare da maida himma ga kananan sana’o’i masu yarin yawa.
Daga nan ya ce ministocin da zai rantsar kwanan nan za su maida himma sosai wajen ganin cewa sun cika alkawurra da maradun da gwamnatin APC ta sha wa al’umma alwashin za ta aiwatar.