Majalisar Dinkin Duniya, UN ta fitar da sanarwar cewa an kashe mutane 35,000 sanadiyyar yakin Boko Haram.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Harkokin Bada Agaji ne ya fitar da wannan sanarwa jiya Asabar.
Cikin wata takarda da ofishin ya fitar jiya Asabar, Majalisar ta ce an kashe mutanen 35,000 ne mafi yawa a jihar Barno, Yobe da kuma Adamawa da wasu garuruwa da rikicin ya yi tsamari a shekarun baya.
UN ta ce wannan kididdiga ta faro ne tun daga farkon fara rikicin na Boko Haram, colin 2009 zuwa yanzu.
Majalisar ta Dinkin Duniya ta kuma ce a cikin wadannan shekaru 10, an kashe ma’aikatan jinkai da agaji har 37.
Wannan bayani ya fitowa ranar da Majalisar ke Jimamin Zagayowar Ranar Ma’aikatan Agaji da Jinkai ta Duniya.
“Mun taru a nan domin tunawa da kuma jimamin ma’aikatan agaji 37 da Boko Haram suka kashe a cikin shekaru goma, tun farkon fara kashe-kashen a 2009.
“Mu na kuma nuna alhinin mu tare da iyalai, abokan da dangin wadanda aka kashe din, da kuma kara taya marayun da aka mutu aka bari alhini da jimami.
“Har ilana yau hankulan mu kuma na kan wadanda ke tsare a hannun Boko Haram da aka yi garkuwa da su, da ma wadanda suka bace babu amo ba labari har yau.
“A wannan rana, mu na so duniya ta sani cewa batun rikicin dandazon masu gudun hijira da ke zaune ko rayuwa a cikin halin kunci a yankin Arewa maso Gabas, babu ranar magance matsalar.”
Daga nan sanarwar ta ce kashe-kashen sun kara kamari ne saboda a yakin Boko Haram ba a bin ka’idar dokokin da Majalisar Dinkin Duniya ta gindaya, ta yadda har mata da kananan yara ake kashewa tare da sace su.