Boko Haram sun yi wa kananan hukumomin Magumeri da Gubio diran mikiya ranar Laraba inda suka kwace ikon kananan hukumomin.
Mazauna wadannan kananan hukumomi na nan a zagaye da mayakan Boko Haram din sannan suna cikin tashin hankali babu halin fita ko kuma gudu domin ficewa daga wadannan garuruwa.
A karamar hukumar Gubio, Boko Haram sun rika barin wuta tun daga karfe 5:30 na Yammacin Laraba har zuwa karfe 2:00 na safiyar Alhamis sannan sun jidi abinci, magunguna, fetur da duk wani abin amfani da suke bukata.
Bayan haka wasu gungun ‘yan Boko Haram dabam suma a daidai wannan lokaci sun far wa karamar hukumar Magumeri. Anan ma bude wuta suka yi suka karbe ikon wannan karamar hukuma kwata-kwata. Isan su Magumeri ke da wuya sai suka far wa hedikwatar karamar hukumar suka cinna mata wuta sannan suke rika bi suna kona asibitoci da dakunan shan magani dake karamar hukumar da dai sauransu.
Idan ba a manta ba, makonni biyu da suka gabata ne Boko Haram suka far wa barikin sojoji da ke Gubio. A wannan hari Boko Haram sun arce da motocin yaki da dama da manya-manyan makamai.
Kakakin rundunar Soji, Sagir Musa bai amsa waya ba da aka nemi samun karin baya ni a akan abinda yakr faruwa.