Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya a harin Bariki

0

A daidai ana shirye-shiryen bukukuwan babban Sallah, ranar Asabar, Boko Haram suka afkawa barikin sojoji dake Gubio, jihar Barno inda suka sojojin Najeriya.

Majiyar mu ta shaida mana cewa duk da sojojin sun yi kokarin fatattakar Boko Haram din abin bai yiwu ba haka suka arce bayan sun kashe wasu sojojin.

Wani kwamandan sojojin ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa yanzu fa babu barikin sojoji ko daya a garuruwan Gubio, Magumeri da Kareto kenan da hakan barazana ce babba ga mazauna wannan yankin.

Harin da aka kaishi da misalin karfe shida na yamman Asabar, yayi sanadiyyar sojoji sannan boko Haram din su arce da manya-manyan motocin yaki da bindigogi da dama.

Akwai rahoton da ya nuna cewa an gano daya daga cikin manyan motocin yakin da suka arce da a cikin daji sun jefar.

Share.

game da Author