BOKO HARAM: An kashe farar hula 27,000 cikin shekara 10 – UN

0

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa akalla an halaka fararen hula 27,000 tsakanin 2009 zuwa 2019, tsawon shekaru 10 aka fafata rikicin Boko Haram.

Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa wannan adadi na mutane 27,000 da ta kiyasta, an halaka su ne a jihohi uku kacal, wato Adamawa, Barno da kuma Yobe.

Babban Jami’in Hukumar Gudanar da Ayyukan Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya, Edward Kallon ne ya bayyana haka ranar Laraba, a lokacin da ake taron jimamin cikar hargitsin Boko Haram shekaru 19 da barkewa.

An gudanar da taro da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja.

Cikin wadanda suka halarci taron har da Gwamnan Jihar Yobe Mala Buni, Babban Daraktan Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Maihaja, Ko’idanatan Ofishin Majalisar Dinkin Duniya, Edem Wosornu da Babbar Jami’ar NINGONET, Josephine Habba.

“Rikicin Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabas ya ci rayuka 27,000 daga 2009 zuwa 2019, tsawon shekaru goma daga barkewar rikicin a wannan yanki na jihohi uku kadai.” Inji Kallon.

Ya kara da cewa Majalisar Dikin Duniya ta bakin cikin wannan kashe-kashe da ke faruwa, wanda musamman tanuna damuwar yadda ya ci har da rayukan ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya da kuma yin garkuwa da wasun su da yawa.

Kwanan nan ma sai da PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka yi garkuwa da wasu ma’aikatan Kungiyar Agaji Ga Mayunwata su shida masu aiki a karkashin kungiyar ta Action Against Hunger a Jihar Barno.

Sannan kuma ko cikin makon da ya bagata Boko Haram sun bindige mutane 60 a kauye daya a Jihar Barno.

Ambaliyar Karin ‘Yan Gudun Hijra

Majalisar Dinkin Duniya ta damu kwarai da yadda aka kara samun yawan masu gudun hijira har su 130,000 a cikin ‘yan watannin baya.

Wadannan sabbin masu gudun hijira wadanda aka raba ne da muhallin su a garuruwa da kauyukan su daban-daban ne.

“Duk da cewa mu na fama da kalubale da dama, bugu da kari kuma akwai mutane milyan 1.7 ‘yan Najeriya masu neman agajin tallafi, su ma wadannan sabbin masu gudun hijira su 130,000 ba za mu juya musu baya ba.”

Ya ce majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyi sun rika ciyar da mutane milyan biyar, yayin da akwi kusan milyan biyu wadanda aka kora daga garuruwan su, da ke zaune a matsugunan sansanin masu gudun hijira.

Ya ci gaba da bayanin irin fannonin da UN ke kai dauki da agaji da tattafi, ciki har da gina matsugunai a sansanonin gudun hijira.

Share.

game da Author