BIDIYO: Yadda sojoji suka kashe ’yan sanda, suka balle min ankwa na tsere – Hamisu Wadume

0

Bayan an yi nasarar kama Hamisu Wadume a Jihar Kano, ya shaida wa jami’an ‘yan sanda yadda sojoji suka bude wa jami’an ‘yan sandan IRS wuta, suka kashe su, sannan kuma suka balle masa ankwa, suka sake shi ya tsere.

Ya yi wannan bayanin ne a hedikwatar su da ke Lious Edet House, a Abuja, bayan an kama shi ranar Litinin da dare, sannan aka wuce da shi Abuja yau Talata da rana.

A hedikwatar Abuja ce ya yi wannan bayanin a yau Talata.

Bayanin da ya yi wa jami’an ‘yan sanda a yau Talata ya yi daidai da zargin da ‘yan sanda suka yi cewa sojoji ne suka bude musu wuta domin su hana a kama Hamisu Wadume ne, wanda ake zargin cewa da sani wasu jami’an sojoji kuma da daurin gindin su ya ke yin garkuwa da mutane.

Wadume wanda ya yi bayani da Hausa, ya ce sojoji ne suka kwance masa ankwa bayan sun kashe ‘yan sandan da suka kamo shi, sannan suka bar shi ya tsere.

“Tun lokacin da na tsere ina boye ne a wani wuri, har zuwa yanzu da ‘yan sanda suka sake kamo ni.” Inji Hamisu.

An kama Hamisu Wadume a Jihar Kano, kamar yadda jan sanda suka bayyana.

Sufeto Janar Muhammed Adamu ya bayyana cewa kama Wadume zai iya bada nasarar kama wasu gungun masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.

Share.

game da Author