BIDIYO: Yadda mahara suka far wa garin Wurma suka tafi da mutane 49 – Maigari Mustapha

0

Maigarin Wurma Alhaji Mustapha Muhammad dake jihar Katsina ya bayyana yadda mahara suka farwa garin Wurma suka sace na sata sannan suka waske da mutane har 49 a wannan Kauye.

Maigari Mustapha ya bayyana cewa yana cikin barci a gidansa sai yaji harbin bindiga ta-ko-ina daga nan ne ya farka a gigice.

Bayan ya farka ne fa sai wasu daga cikin masu garkuwan suka shiga gidansa har dakinsa inda suka kwashi na kwasa sannan suka yi tafiyarsu.

Maigari yace maharan sun kai akalla 300 kuma dukkan su dauke da manyan bindigogi.

Yace akalla mutane 49 ne suka bace, saidai zuwa yau an sako mutane 11 cikin su.

Share.

game da Author